Firaministan Tunisiya ya yi kira gaggawa | Labarai | DW | 07.02.2013
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Firaministan Tunisiya ya yi kira gaggawa

Firaministan kasar Tunisiya Hamadi Jebali ya bayyana kiran zabe cikin gaggawa

Firaministan kasar Tunisiya Hamadi Jebali ya yi alkawarin rusa majalisar dokoki, domin kiran zabe cikin gaggawa, wannan sa'o'i kadan bayan kisan madugun 'yan adawan kasar abun da ya haifar da zanga zanga.

Yayin jawabi ta tashar talabijin Firaminista Jebali ya ce zai kafa gwamnatin da ta kunshi kwararru ta wucin gadi, zuwa lokacin da za a gudanar da zabuka.

Wannan ya zo lokacin da 'yan sandan kasar kasar ke artabu da masu zanga zanga sanadiyar kisan Chokri Belaid, madagun 'yan adawa da aka harbe a wannan Laraban da ta gabata. Tuni shugaban kasar ta Tunisiya Moncef Marzouki ya yi tir da wannan kisa. A kasar aka fara juyin juyin hali kasashen Larabawa cikin shekara ta 2011, inda masu zanga zanga suka kawo karshen gwamnatin Zine el-Abidine Ben Ali.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Halima Balaraba Abbas

 • Kwanan wata 07.02.2013
 • Mawallafi Mark Hallam
 • Muhimman kalmomi Tunisia
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/17ZzM
 • Kwanan wata 07.02.2013
 • Mawallafi Mark Hallam
 • Muhimman kalmomi Tunisia
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/17ZzM