Firaministan Mongolia ya yi murabus | Labarai | DW | 21.01.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Firaministan Mongolia ya yi murabus

Zanga-zangar adawa da matakan cutar coronavirus ta yi awon gaba da kujerar firaministan kasar Mongolia Khurelsukh Ukhnaa. 

Wannan na zuwa ne bayan da alummar kasar da ke yankin Asiya suka yi wani bore bayan samun wani rahoton bidiyo da ya nuna yadda aka dauki wata mata da ta haihu cibiyar kulla da masu cutar corona ba tare da wani kyakyawan sutura ba a cikin yanayi ma tsakancin sanyi.

Lamarin da ya sa Firaministan Khurelsukh Ukhnaa daukar laifin a kanshi da kuma yin murabus.

Da yake jawabi ga ya ce an yi kuskure ga yadda aka fidda matar, kuma a matsayina na shugaba dole na dauki alhakin hakan.