Firaministan Mali ya yi murabus daga muƙaminsa | Labarai | DW | 11.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Firaministan Mali ya yi murabus daga muƙaminsa

A wata sanarwa da gidan talabin ɗin ƙasar ta karanto, Mr. Diarra ya ce ya sauka daga gadon mulki tare da ministocinsa, sai dai bai bayyana dalilansa na yin hakan ba.

epa02792849 Cheik Modibo Diarra, chairman of Microsoft Africa attends a press conference to present the George Arthur Forrest foundation, in Brussels, Belgium, 24 June 2011. The foundation wants to contribute to a good economic, social and political government in Africa. EPA/NICOLAS MAETERLINCK ***BELGIUM OUT*** +++(c) dpa - Bildfunk+++

Mali Ministerpräsident Scheich Modibo Diarra

Wannan murabus ɗin na Mr. Diarra ya zo ne jim kaɗan bayan tsare shi da sojin ƙasar wanda su ka shirya juyin mulki watan Maris ɗin da ya gabata, su ka yi lokacin da tsohon Firaminstan ke ƙoƙarin ficewa daga ƙasar zuwa Faransa.

Da ya ke magana jim kaɗan bayan saukar Mr. Diarra daga muƙaminsa, mai magana da yawun rundunar sojin da su ka yi juyin mulki a ƙasar Bakary Mariko ya ce kama tsohon Firaministan ba wai ya na nufin wani sabon juyin mulki ba, inda ya ƙara da cewar shugaban ƙasar na nan daram kan iko.

Sojin dai sun ce sun kame Mr. Diarra ne saboda abin da su ka kira ƙoƙarin dagula lamura a ƙasar kuma sun ce yanzu haka su na tsare da shi a wani barikinsu da ke Kati, a wajen garin Bamako fadar gwamnatin ƙasar.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Yahouza Sadissou Madobi