Firaministan Libya ya tsallake rijiya da baya | Labarai | DW | 27.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Firaministan Libya ya tsallake rijiya da baya

Masu zanga-zangar sun yi barazanar kisan firaministan kasar tare da bukatar ganin 'yan majalisar kasar sun cire shi daga kujerarsa. abin da bangaren gwamnati ke cewa bita da kulli ne na siyasa.

Abdullah al-Thinni

Firaminista Abdullah al-Thinni na Libya

Wasu 'yan bindiga a kasar Libya sun yi yunkurin sace Firaministan kasar da al'ummomin kasa da kasa suka amince da shi, a lokacin da ya ke kan hanyarsa ta zuwa filin tashi da saukar jiragen sama na gabashin Tabrouk a ranar Talata kamar yadda mai magana da yawun gwamnatin kasar ya bayyana.

Arish Said da ke zama mai magana da yawun gwamnatin kasar ta Libya ya ce an kai farmaki ne ga jerin gwanon motocin firaminista Abdullah al-Thinni, harin da yayi sanadin raunata daya daga cikin masu tsaronsa , babu wanda ya rasa ransa, sai dai sun sha da kyar.

Said ya ce kafin kai wannan hari wasu masu dauke da bindigar sun taru a gaban gidan wakilan gwamnatin kasar da ke a birnin Tabrouk, inda suke ta harbi a samaniya tare da bukatar al-thinni ya sauka daga kujerarsa.

Masu zanga-zangar har-ila-yau sun yi barazanar kisan firaministan kasar tare da bukatar ganin 'yan majalisar kasar sun cire shi daga kujerarsa .

A cewar mai magana da yawun gwamnatin kasar wadannan masu zanga-zanga wasu masu fada aji ne na bangaren 'yan siyasa a birnin na Tabrouk suka dauki nauyinsu, sai dai bai yi karin haske ba kan wadanda a ke zargi.