Firaministan Lesotho ya koma gida | Labarai | DW | 03.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Firaministan Lesotho ya koma gida

Thomas Thabane ya koma gida daga Afirka ta Kudu inda ya yi hijira kwanaki huɗu bayan juyin mulkin da sojoji suka yi masa.

Wani mai bai wa firaminista shawara da ke tare da shi, ya shaida wa kamfanin dilancin labarai na Faransa AFP. Cewar tuni har sun isa a fadar shugaban ƙasar tare da rakiyar wasu sojojin Afika ta Kudu da kuma wasu 'yan sandar na Lesotho.

An dai kai ga cimma wannan matsaya ce ta komawar shugaban gwamnatin bayan da Ƙungiyar SADEC ta ƙasashen gabashin Afirka ta shiga tsakani. A ranar Asabar da ta gabata ne sojoji na ƙasar ta Lesotho suka kifar da gamnatin mista Thabane.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu