Firaministan Lesotho ya gurfana gaban kotu | Labarai | DW | 24.02.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Firaministan Lesotho ya gurfana gaban kotu

Firaministan Lesotho Thomas Thabane ya gurfana gaban wata kotu a yau domin amsa tuhuma da ake yi masa ta kisan tsohuwar mai dakinsa a cikin watan Yunin shekarar 2017 a lokacin da suke kokarin rabuwa.

Masu aiko da rahotanni suka ce shugaban ya isa kotun ce da ke babban birnin kasar wato Maseru tare da matarsa ta yanzu wadda ya aura watanni biyu bayan rasuwar tsohuwar matarsa.

Tun a ranar Asabar din da ta gabata ce dai Thabane dan shekaru 80 da haihuwa ya kamata ya gurfana gaban kuliya, sai dai bai halarci zaman kotun ba, inda 'yan sanda suka yi barazanar kama shi amma hadimansa sun ce rashin lafiya ce ta hana shi zuwa kotun, hasalima ya je Afirka ta Kudu ne neman magani.