1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Firaministan kasar Mali ya ajiye aiki

Zulaiha Abubakar
April 19, 2019

Firaministan Mali Soumeylou Boubeye Maïga tare da majalisar gudanarwar kasar sun sanar da ajiye aiki nan take sakamakon tabarbarewar tsaro a kasar. Tuni shugaban kasa Ibrahim Boubacar keita ya amince da wannan mataki.

https://p.dw.com/p/3H4C1
Mali - Soumeylou Boubèye Maïga
Hoto: picture alliance/dpa/F. Alvarado

Murabus din Firaministan Mali ya zo makonni hudu bayan kisan gillar da wasu 'yan kato da gora daga wata kabila a kasar suka yi wa Fulani makiyaya wadanda yawansu ya kai 160, kisan kan da ya girgiza kasar baki daya. Dama wasu hare-haren sun gudana a bangarorin kasar wadanda suka hada da wani hari da yayi sanadiyyar rasa rayukan sojoji 23. 

Tun da farko sai da zauren majalisar dokokin kasar Mali ya tabka zazzafar muhawara kan gazawar gwamnatin kasar wajen raba 'yan ta'adda da makamai da kuma dakile akidar tsattsauran ra'ayin addini a fadin kasar. Dakarun kwantar da tarzoma na Majalisar Dinkin Duniya da yawansu ya kai dubu 16 tare da sojojin kasashen Jamus da Faransa na ci gaba da aikin tsaro a kasar ta Mali.