1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Firaministan kasar Haiti ya yi murabus

March 12, 2024

Tun daga shekara ta 2021 Henry ke rike da mukamin da aka nada shi ba tare da gudanar da zabe ba bayan kisan gillar da aka yi wa shugaban kasar Haitin da ya gabata.

https://p.dw.com/p/4dPcD
Hoto: Andrew Kasuku/AP Photo/picture alliance

Firaministan kasar Haiti Ariel Henry ya yi murabus daga mukaminsa bayan makonnin da aka kwashe ana tashin hankali a wannan kasa da ke yankin Caribbean. Tashin-tashinar da ta wakana dai ta kai ga fusatattun mutane na lalata kadarorin gwamnati tare da kokarin rasa bin doka da oda.

Sai dai rahotanni na nuna cewa firaministan zai jirkinta dakatar da zuwa ofishar sai an kafa sabuwar gwamnati.

Haiti dai na cikin kasashen yankin Caribbean da suka yi kaurin suna wajen ayyukan'yan daba, inda a galibi zanga-zangar lumana domin nuna fushi kan rikide zuwa tashin hankali ta hanyar tsallake tanadin da dokoki suka wajen nuna fusata.