Firaministan kasar Jordan ya sauka daga mulki
June 4, 2018Talla
A baya dai matakan tsuke bakin aljihun da Firaministan kasar Hani Al-Mulki ya dauka don samarwa kasar ta Jordan karin kudin shiga, wadanda suka hada da rage kudin tallafin gwamnati a kan wasu muhimman kayan masarufi da suka hada da biredi a fadin kasar, na daga cikin abubuwan da suka jawo masa bakin jini, lamarin da ya haifar da wata zanga-zanga irinta ta farko a kasar.
Al'umma kasar sun bayyana kin jinin karin kudin haraji tare kuma da kiran tsohon Firaminista a kan ya sauka daga mulki sakamakon zarginsa da suka yi da gazawa wajen shugabanci.
Shirye-shirye sun yi nisa don kaddamar da sabuwar gwamnati a kasar kamar yadda Sarki Abdullah Al-Hussein ya bada umarni.