1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Abiy Ahmed ya fara jagorancin yaki

Suleiman Babayo AT Bala
November 26, 2021

An nuna hotunan Firaminista Abiy Ahmed na kasar Habasha inda ya fara jagorancin yakin da sojojin kasar ke yi da mayakan kungiyar TPLF.

https://p.dw.com/p/43YPc
Äthiopien Tigray Krise
Hoto: AP Photo/picture alliance

Firaminista Abiy Ahmed na kasar Habasha ya bayyana karon farko a fagen daga a yakin da dakarun kasar ke fafatawa da mayakan kungiyar TPLF na yankin Tigray. Kafofin yada labarai sun nuna hotunan firamnistan cikin kayan sojoji, inda yake cewa wurin da suke tsaye shi ne na farko da suka kwace daga hannun mayakan na TPLF.

Firaminista Abiy Ahmed wanda ya samu lambar kyautar zaman lafiya ta Nobel ya ce za su binne makiya kasar.

Kungiyoyin kasashen duniya musamman kungiyar tarayyar Afirka ta kasar Amirka suna ci gaba da neman ganin an samu yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin bangarorin yayin da Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin yakin na shekara guda ya jefa fiye da mutanen milyan tara cikin matsanancin yunwa, kuma kullum ana kara samun mutane da ke shiga mawuyacin hali.