Firaministan Guinea Bisau ya yi murabus | Labarai | DW | 09.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Firaministan Guinea Bisau ya yi murabus

Kotun tsarin milkin Guinea Bisau ta ce nadinsa a kan wannan mukami ya Saba wa Kundin tsarin milkin kasar. Saboda haka ne Firaministan ya sauka daga mukaminsa.

Baciro Dja wanda dama a wannan Litanin ce ya kaddamar da majalisar ministocinsa, ya shaida wa manema labarai wannan mataki bayan da a cewarsa Shugaban kasar Jose Mario Vaz ya sanar da shi cewa kotun tsarin milkin kasar ta ce nadin da aka yi masa a kan wannan mukami a cikin watan Agustan da ya gabata ya saba wa kundin tsarin milkin Guinea Bisau.

Kotun ta ce kundin tsarin milkin kasar ya tanadi cewa jam'iyyar da ta lashe zaben 'yan majalisar dokoki ce ke da hurumin daukar mukamin Firaminista. Babbar jam'iyyar adawar kasar ta Guinea Bisau wacce ke da rinjaye a majalissar dokokin kasar ce ta shigar da kara a gaban kotun , inda ta kalubalanci matakin shugaban kasar na sauke Domingo Simoes Pereira na bangaren adawa daga mukamin Firaminista domin maye gurbinsa da Baciro Dja wanda kotun tsarin milkin ta yi watsi da nadin nasa a yanzu.