Firaminista ya ajiye aiki | Labarai | DW | 27.04.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Firaminista ya ajiye aiki

Firaministan kasar Koriya ta Kudu ya mika takardar ajiye aiki saboda yadda gwamnati ta tunkari hatsarin jirgin ruwa da ya hallaka mutane masu yawa

Firaminista Chung Hong-won ya mika takardar ajiye aiki, saboda yadda gwamnati ta tunkari hatsarin jirgin ruwa da ya hallaka mutane 187, yayin da masu aikin ceto ke ci gaba da neman sauran mutane 115 mafi yawa yara 'yan makaranta.

Firaministan ya ajiye aikin dai dai lokacin da gwamnatin ke shan suka biya yadda ta tunkari lamarin. Kawo yanzu Shugaba Park Geun-hye ba ta bayyana amincewa da murabus din ba tukunna.

Masu gabatar da kara na kasar ta Koriya ta Kudu sun cafke daukacin ma'aikatan jirgin ruwan da ya yi hatsarin 15, kan zargin sakaci da aiki.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Usman Shehu Usman