Firaminista Olmert ya yi fatan za´a kira taron GTT kwanan nan | Labarai | DW | 19.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Firaminista Olmert ya yi fatan za´a kira taron GTT kwanan nan

FM Isra´ila Ehud Olmert ya ce a shirye ya ke ya halarci wani taron koli na yankin GTT don ganawa da shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas. Bayan tattaunawar da yayi da FM Birtaniya Tony Blair Olmert ya ce yana fata za´a shirya wannan taron koli nan ba da dadewa ba. Da farko kuwa FM Blair ya gana da shugaban Falasdinawan Mahmud Abbas a birnin Ramallah. Abbas dai na samun goyo baya ga shirin sa na gudanar da sabon zabe na gaban lokaci a yankunan Falasdinawa.