FIFA: Infantino zai mutunta matakin bincike | Labarai | DW | 03.08.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

FIFA: Infantino zai mutunta matakin bincike

Hukumar kwallon kafa ta duniya wato FIFA ta ja hankalin gwamnatin Switzerland bayan gurfanar da shugabanta Gianni Infantino

Shugaban Hhukumar kwallon kafa ta duniya FIFA Gianni Infantino ya yi alkawarin marataba dukkan hukuncin da kwamitin da'a na hukumar zai yanke bayan da hukumomin Switzerland suka fara binciken zargin aikata manyan laifuka akansa.

Mai gabatar da kara na musamman na kasar Switzerland ya kaddamar da bincike akan zargin hadin baki tsakanin babban lauyan gwamnatin kasar Michael Lauber da kuma Infantino zargin da dukkaninsu suka musanta.