1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fatan sabuwar dangantakar Jamus da Israila

January 21, 2013

Tsamin dangantakar Jamus da Israila kan manufofin Israila a yankunan Palesdinawa a daidai lokacin da kasar ta Isra'ila ke gudanar da zaben gama gari.

https://p.dw.com/p/17OMg
Hoto: dapd

Ranar Talata, za'a gudanar da sabon zaben majalisar dokoki a kasar Israila. Pirayim minista ma ci, Benjamin Netanyahu, yana iya sakin jikinsa, ya kuma kada kueri'ar sa a goben ba tareda nuna wata damuwa ba, saboda ra'ayoyin jama'a da aka jik afin zaben sun nuna cewar Pirayim ministan mai barin gado, shine kuma za'a zaba yaci gaba da mulki. Jam'iyar Likud Beitrenu mai matsanancin ra'ayi ta Benjamin Netanyahu tare da abokin hadin gwiwarsa, tsohon ministan harkokin waje, Avigdor Liebermann, an yi imanin zasu sami akalla kashi kashi daya cikin kashi ukku na kuri'un da za'a kada.

To sai dai Netanyahu zai yi fama da adawa daga wasu jam'iyun masu ra'ayin rikau, misali daga jam'iyar Yahudawa mai matsanancin ra'ayin addinin Yahudanci, karkashin jagorancin Neftali Bennett, wadda ke iya zama jam'iya ta ukku mafi girma a zaben na Israila, bayan jam'iyar Labour. Abin da zai zama mai matukar muhimmanci a game da matakan neman zaman lafioya a gabas ta tsakiya, shine ko a bayan zaben na ranar Talata, Netanyahu zai kyale Bennett ya matsa masa lambar kara tsananta manufofinsa, ko kuma Pirayim ministan zai amince da hadin gwiwa tare da jam'iyu masu sassaucin ra'ayi da basu dogara sosai da manufofi na addini ba. Gwamnatin Jamus tun kafin zaben ta nuna damuwa a game da yadda sakamakonsa zai shafi batun neman zaman lafiya da Palesdinawa. Shugaban kwamitin harkoikn waje a majalisar dokokin taraiya, Ruprecht Polenz yake cewa:

Zamu yi kokarin sake kusantar da Israila da Palessdinawa, yadda za'a kai ga samun kammala tattaunawarsu, kuma a lokaci guda muna duba, tare da matukar damuwa, idan jam'iyun siyasar Israila suka shiga kampe tare da alkawarin maida dukkanin yankunan Palesdinawa da suka mamaye a yammacin kogin Jordan su zama mallakin Israila gaba dayanua, daga baya kuma su maida yankin na matsugunan Yahudawa. Gwamnatin taraiya ko a da can ma tasha sukan manufofin kakkafa matsugunan Yahudawa na Israila, saboda wannan tsari ne dake yin cikas a kokarin kafa kasar Palesdinawa kafada da kafada da Israila, kuma watakila ma idan aka ci gaba dashi, zai hana shirin gaba daya.

Angela Merkel und Benjamin Netanyahu
Benjamin Netanyahu da shugabar gwamnatin Jamus, Angela MerkelHoto: Getty Images

Bisa al'ada, Jamus tana da kyakkyawar danganta tsakaninta da Israila, kuma tana ganin alhakin tabbatar da tsaron Israila abune da ya rataya a wuyanta. Kasashen biyu sukan gudanar da taro na hadin gwiwa na tuntubar juna akalla sau daya a shekara tun daga shekara ta 2008, inda a bana ma ake sa ran bayan zaben na Israila, majalisar dokokin Jamus ta Bundestag da majaisar Israila ta Knesset zasu cimma yarjejeniyar hadin kai a aiyukan su na majalisun dokoki, duk kuwa irin sakamakon da za'a samu a zaben na Israila.

Duk da haka dangantaka tsakanin Israila da Jamus a yanzu dai tana daga da yan matsaloli. Bayan da Jamus tayi rowar kuri'arta a majalisar dinkin duniya game da baiwa Palesdinawa kujerar yan kallo a majalisar, Pirayim minista Benjamin Netanyahu ya baiyana rashin jin dadinsa. Amma kamar yadda tsohon jakadan Israila a nan Jamus, Avi Primor ya nunar, lokacin hira da DW, akwai mutane da dama a Jamus dake bakin cikin take-taken Israila.

A ra'ayi na, bai kamata Jamus tayi shisshigi a abubuwan dake gudana a Israila ba, amma a bayan zabe da kafa gwamnatin hadin gwiwa, tana iya shimfida sharadinta: idan har kuna son goyon bayanmu, to kuwa tilas manufofinku na siyasa su dace da namu, saboda halin da ake ciki a gabas ta tsakiya, al'amari ne da ya shafi Jamus da nahiyar Turai baki daya.

Musamman Jamus tafi baiyana rashin jin dadinta ne tattare da manufofin kakkafa matsugunan Yahudawa da Israila take yi. Ruprecht Polenz, shugaban kwamitin harkokin waje a majalisar dokoki yace hakan yana kawo cikas a kokarin kafa yantacciyar kasar Palesdinawa da zata zauna kusa da Israila, abin da ma yace Israilan ita kanta zata ci gajiyarsa, saboda ita ce kadai hanyar da zata tabbatar Israilan ta zauna a yanayin tsaro da kwanciyar hankali da makwabtanta.

Israel Siedlungsbau Jerusalem Siedlung Maale Adumim
Daya daga cikin matsugunan Yahudawa a Maale AdumimHoto: picture alliance / landov