1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fashewar bam a Somaliya

January 2, 2014

Kungiyar al-Shabab ta dauki alhakin harin bam da ya janyi mutuwar jama'a a kasar Somaliya.

https://p.dw.com/p/1AkCw
Somalia Mogadischu Jazira Hotel Anschlag
Hoto: Reuters

Akalla mutane 8 ne suka mutu sakamakon tarwatsewar bam a cikin wasu motoci a kasar Somaliya. Bama baman dai sun fashe ne a wasu motoci biyu da ke ajiye a wajen wani hotel mai suna Jazeera da ke kusa da filin sauka da tashin jiragen saman Mogadishu, babban birnin kasar ta Somaliya a wannan Larabar (01. 01. 13). Rahotanni kuma sun nunar da cewar, harbe harbe sun biyo bayan tashin bama baman a tsakanin maharan da kuma jami'an tsaro. Kungiyar al-Shabab ta kasar Somaliya, wadda ke da alaka da kungiyar al-Qa'ida ce dai ta dauki nauyin kaddamar da harin. Idan za a iya tunawa dai, tun a shekara ta 2011 ne dakarun tsaro suka fatattaki kungiyar daga Mogadishu, amma har ya zuwa yanzu, ita ce ke da iko da wasu yankunan da ke kudanci da kuma gabashin kasar ta Somaliya.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu