1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus za ta taimaki Afirka ta Kudu kan corona

Abdoulaye Mamane Amadou
May 28, 2021

Ministan lafiya na Jamus Jens Spahn ya yi wa kasar a Afirka ta Kudu albishir na ba da gudunmawa a fannin fasahohin zamani domin soma aikin samar da allurar covid-19 a kasar ta nahiyar Afirka.

https://p.dw.com/p/3u8ZZ
Südafrika Corona-Gesprächen | Besuch von Bundesgesundheitsminister Spahn
Hoto: Christoph Soeder/dpa/picture alliance

A cewarsa Minista Spahn dai kwararru a fannin samar da rigakafi na Jamus a shirye suke da su tallafa wa duk wani yunkuri na samar da alluarar rigakafin corona a duniya. 

Ya ce "Kullun muna fada cewa abu mai muhimmanci ba shi ne adadin wadanda suka kamu ba, abin da yake da muhimmanci shi ne karfin samar da allurar rigakafin. Da kuma hadin da ake bukata a wannan bangaren, ma'ana samar da allurar rigakafin na bukatar kwarewa da kuma hadin kai daga kowanne bangare." 

Ministan kiwon lafiyar na Jamus ya yi wannan jawabin ne yayin ganawarasa da takwaransa na Afirka ta Kudun Zweli Mkhize.