Fargabar rashin nasarar zabe a Mali | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 30.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Fargabar rashin nasarar zabe a Mali

Tashe-tashen hankula da garkuwa da jami'an zabe hade da ayukan 'yan fashi a biranen arewacin kasar na barazana ga zaben shugaban kasar Mali.

A wannan Lahadi ake gudanar da zaben shugaban kasa a Mali sai dai a labarin da ta buga mai taken mummunar dama ga zabukan na Mali, jaridar Die Tageszeitung cewa ta yi:

"A ranar Lahadi al'ummar ke zaben sabon shugaba kasa, sai dai ba wanda ke da imanin cewa zaben zai gudana cikin wani yanayi na gaskiya da adalci musamman a arewacin kasar inda ake fama da tashe-tashen hankula. Kusan shekara daya da rabi ke nan kasar ta Mali ba ta da wani halastaccen shugaba da aka zaba ta hanyar demokradiyya tun bayan juyin mulkin ranar 22 ga watan Maris na shekara ta 2012. Kasar na fama da karancin ababen more rayuwa, ga kuma rashin tsaro da ya zama ruwan dare a arewacin kasar. Wani abin da ya fi damun mazauna wannan yanki shi ne rigingimun baya-bayan nan inda a makon da ya gabata aka hallaka mutane hudu a wata arangama tsakanin magoya bayan kungiyar MNLA da wasu mutane da MNLA ta zarga da goya wa gwamnatin birnin Bamako baya. A cikin irin wannan yanayi da wuya a iya shirya wani zabe da zai samu karbuwa."

Magudin zabe tun gabanin kada kuri'a a Zimbabwe

Har yanzu muna a kan batun zabe ne a wannan karon a Zimbabwe wadda ita ma za ta gudanar da zabuka a ranar 31 ga watannan na Yuli. A labarin da ta buga jaridar Die Zeit cewa ta yi:

Bildnummer: 55272682 Datum: 18.04.2011 Copyright: imago/Xinhua (110418) -- HARARE, April 18, 2011 (Xinhua) -- Zimbabwean president Robert Mugabe(L) greets Zimbabwean Prime Minister Morgan Tsvangirai (R) upon his arrival at the 31st Independence celebration in Harare on April 18, 2011. (Xinhua/Wan Da) (lj) ZIMBABWE-HARARE-INDEPENDENCE CELEBRATION PUBLICATIONxNOTxINxCHN Politik Gesellschaft Feiertag Unabhängigkeit Unabhängigkeitstag jahrestag kbdig xub 2011 quadrat premiumd o0 People Bildnummer 55272682 Date 18 04 2011 Copyright Imago XINHUA Harare April 18 2011 XINHUA Zimbabwean President Robert Mugabe l greets Zimbabwean Prime Ministers Morgan Tsvangirai r UPON His Arrival AT The 31st Independence Celebration in Harare ON April 18 2011 XINHUA Wan there LJ Zimbabwe Harare Independence Celebration PUBLICATIONxNOTxINxCHN politics Society Holiday Independence Independence Day Anniversary Kbdig 2011 Square premiumd o0 Celebrities

Mugabe da Tsvangirai

"Shugaba Robert Mugabe ya shirya tsab don tabka sabon magudin zabe, sai dai wani mai fallasa labaran sirri ya gano take-takensa. Jaridar ta ci gaba da cewa bisa al'ada a duk lokacin zabe a Zimbabwe ana tursasa wa 'yan adawa kuma hukuma kan yi aringizon kuri'u wanda a karshe Robert Mugabe ke yin nasara. Sai dai a wannan karon shugaban mai shekaru 89 ba zai iya tabbatar da wannan nasara kai tsaye ba saboda turjiya da yake fuskanta daga cikin magoya bayansa. Wani abin da ya kara jefa shi cikin halin rashin sanin tabbas shi ne wani mai fallasa labari wanda tun wasu watanni kenan yake bankado wasu ababan kunya da gwamnati ke yi kuma yake wallafawa a shafin Facebook. Kawo yanzu dai wannan talaki bai fid da kamaninsa ba. Daga cikin labaran har da karerayin da gwamnati ke yi game da koshin lafiyar Mugabe da makudan kudaden da jam'iyar ZANU-PF ta kashe wajen sayen kuri'un masu zabe."

Jan aiki a gaban sabuwar rundunar zaman lafiya a Kongo

U.N. Secretary-General Ban Ki-moon is escorted by U.N. peacekeepers during his trip in Goma, in the Democratic Republic of Congo's war-torn east, May 23, 2013. Rebels in eastern Congo announced a ceasefire on Thursday in fighting with government troops hours before a visit to the conflict-plagued zone by Ban and World Bank President Jim Yong Kim. REUTERS/Jonny Hogg (DEMOCRATIC REPUBLIC OF CONGO - Tags: POLITICS CIVIL UNREST)

Ban Ki Moon a birnin Goma a cikin watan Mayun 2013

Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung tsokaci ta yi game da tawagar sojojin Majalisar Dinkin Duniya a Kongo. Ta ce yanzu haka sojoji 2000 daga cikin fiye da 3000 sun isa yankin dazuzzuka na gabacin Kongo, amma ba za su saka hulunan kwano masu launi shudi wanda bisa al'ada sojojin Majalisar dake aikin wanzar da zaman lafiya ke amfani da su ba. An dauki wannan mataki ne don a kare su daga hare-haren masu fada da juna a yankin wato sojojin gwammati da kuma 'yan tawaye. Jaridar ta ce wannan wani sauyin manufa ne ga ka'idojin girke dakarun Majalisar Dinkin Duniya wadanda aikinsu shi ne hana aukuwar rikici amma ba amfani da karfi ba. Sai dai a wannan karo abubuwa za su canja domin an ba wa sabuwar rundunar ikon tsoma baki a cikin rikicin Kongo.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu