Fargabar fuskantar matsananciyar yunwa a Sudan ta Kudu | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 25.04.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Fargabar fuskantar matsananciyar yunwa a Sudan ta Kudu

Yakin da ke ci gaba tsakanin gwamnati da 'yan tawaye a Sudan ta Kudu yana barazana ga aikin gona abin da ka iya jefa kasar cikin mummunar masifar yunwa.

Bari mu fara da jaridar Süddeutsche Zeitung wadda ta mayar hankali a kan kasar Sudan ta Kudu tana mai cewa kasar ta doshi hanyar fadawa matsalar yunwa saboda yakin basasan da take fuskanta.

"Kamata ya yi yanzu an fara shuki gadan gadan a Sudan ta Kudu kuma kananan manoma da 'yan kasar su kimanin miliyan tara suka dogara kansu, sun fara zuwa kasuwanni don sayen irin shuka kafin saukar damina. To amma a bana abubuwa sun canja, domin tun a wasu watanni ke nan dakarun gwamnati da na 'yan tawaye suke yakar juna, sannan ana cikin zaman fargaba ta fuskantar kisan kare dangi daga bangarorin biyu da ke gaba da juna. Saboda haka babu mai tunanin zuwa gona don yin shuki. Saboda haka gamaiyar kasa da kasa ke yin kashedi cewa idan ba a gaggauta daukar matakai ba, to mutane kusan miliyan daya a kasar ta Sudan ta Kudu ka iya fuskantar matsalar yunwa a cikin watanni kalilan masu zuwa. Asusun taimakon yara na Majalisar Dinkin Duniya wato UNICEF cewa ya yi idan ba a samu ingantuwar halin da fafaren hula ke ciki ba, to kanana yara kimanin dubu 50 'yan kasa da shekaru biyar, za su mutu."

Rashin tabbas ga makomar dalibai a Najeriya

Schule in Nigeria

'Yan makaranta a kudancin Najeriya

Har yanzu babu duriyar ‘yan matan makarantar sakandaren nan da aka yi garkuwa da su a arewa maso gabacin Najeriya inji jaridar Die Tageszeitung sannan sai ta ci gaba da cewa.

„A bayyane yake cewa har yanzu fiye da dalibai ‘yan mata 200 suna hannun ‘yan bindiga da ake zargin ‘ya'yan kungiyar Boko Haram ne, ko da yake ba wanda ya san ainihin gaskiyar abin da ke faruwa da kuma ainihin yawan wadanda suka kubuta daga hannun masu kaifin kishin addinin. A cikin kwanakin da da suka wuce an yi ta ba yin bayanai masu cin karo da juna game da yawan daliban da aka yi garkuwa da su da kuma rashin wani katabus daga hukumomi na ceto su, abin da ke kara harzuka iyayen yara da ma suka yi yunkurin shiga cikin dajin Sambisa inda ake kyautata zato ana tsare da yaran don ceto su. Wannan yanki har izuwa kann iyaka da kasar Kamaru na zama tungar Boko Haram, suna kuma cin karensu babu babbaka a yankin saboda rashin tsaro a wannan yanki.“

Duniya na kau da kai daga ta'asa a Ruwanda

Paul Kagame Präsident Ruanda

Paul Kagame shugaban kasar Ruwanda

Ita kuwa jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung a wannan mako ta leka kasar Ruwanda ne inda ta yi tsokaci game da tsarin kasar da ta ce na rashin adalci ne.

„Don gudun ka da su shiga cikin wata kasada shigen ta Mogadishu, Majalisar Dinkin Duniya da wasu daidaikun kasashe suna kau da ido daga bakin babi na gamaiyar kasa da kasa da fannin diplomasiya a Afirka. Abin mamaki ba wanda ke magana cewa a cikin shekaru 20 da suka wuce tun bayan kisan kare dangi da aka yi wa ‘yan Tutsi a Ruwanda, da kudaden tallafi daga kasashen yamma musamman Amirka, Birtaniya da kuma tarayyar Turai an samar da wani tsari gwamnati maras adalci a Ruwanda. A karkashin shugabancin Paul Kagame ana fatali da hakkin dan Adam, ana tursasa wa ‘yan adawa a wasu lokutan ma ana yi musu kisan gilla. Amma ana sukar irin wannan ta'asar idan suka auku a kasashe irinsu China, Belarus ko Kwango, yayin da a a Ruwanda tun bayan aukuwar kisan kare dangin shekarar 1994, a kaikaice ana tallafa wa wannan ta'asar da kudaden taimakon raya kasa.”

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu