Fargabar daukar HIV a kasar Ostareliya
July 2, 2015Talla
Hukumomin kasar Ostareliya sun ce mutane kimanin dubu11 ne ake fargabar sun dauki kwayoyin cutar HIV a kasar bayan da wasu likitocin hakura su 12 da ke aiki a wani gidan assibitin birnin Sydney suka yi amfani da kayan aikinsu ba tare da sake tsabtace su ba bayan wani aiki da suka yi da su a baya.
Hukumomin kiwon lafiyar kasar ta Ostareliya sun ce sun yi kira ga mutanan kimanin dubu 11 da su kawo kansu a gudanar da bincike domin tantance in har ba su kamu da kwayoyin cutar ta HIV ba.Tuni dai hukumomin suka dauki matakin dakatar da aikin wasu likitocin shida a yayinda aka baiwa sauran shidar damar ci gaba da aikin nasu amma a bisa wasu sharudda.