Farashin danyen man fetur ya kara faduwa | Labarai | DW | 11.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Farashin danyen man fetur ya kara faduwa

Farashin gangar danyen man fetur yana ci gaba da faduwa a kasuwar duniya

Farashin gangar danyen man fetur ya kara faduwa a kasuwar duniya da kimanin Centi 58, inda yanzu ake sayar da kowace ganga a kan dalar Amirka 60 da Centi 85. Haka ya zo lokacin da aka fara sa ran yuwuwar tashin farashin man.

Kasashen masu arzikin man fetur suna sa ran nan gaba cikin wannan shekara farashin man zai haura, inda tuni faduwar farashin ya shafi kasafin kudin kasashen, saboda raguwar kudaden shiga.

Kungiyar kasashen masu arzikin man fetur ta OPEC, da ta saba rage yawan danyen man fetur da ake kai wa kasuwa idan farashi ya fadi, a wannan karo ba ta dauki matakin ba, inda aka bar kasashe su ci gaba da fitar da man kamar yadda aka saba. Yanzu haka kasashen na fitar da ganga milyan 30 kowace rana.