Farashin danyen man fetur na ci gaba da faduwa | Labarai | DW | 08.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Farashin danyen man fetur na ci gaba da faduwa

Faduwa da ake samu na farashin danyen man fetur tsakanin kasashen duniya na kassara tattalin arzikin kasashe masu dogara da man fetur.

Farashin danyen man fetur ya yi faduwar da ba a taba gani ba cikin fiye da shekaru 10, inda ake sayar da kowani ganga dayen man a kan dalar Amirka 33 da centi 84. Haka ya zama farashi mafi karanci tun shekara ta 2004.

Akwai damuwa na cewa farashin kai kara sauka abin da ke shafan tattalin arziki kasashe masu dogaro kan man fetur. Kasashen masu arzikin man fetur na kungiyar OPEC za su gudanar da taro a farkon watan shida na Yuni, domin duba yuwuwar daukar wani matakin farfado da farashin na danyen man, sai dai akwai sabani na siyasa tsakanin kasashen kan zabtare man da ake kai wa kasuwa.