1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa za ta janye sojinta daga Mali

Zainab Mohammed Abubakar
May 30, 2021

Shugaba Macron na Faransa ya ce, yana la'akari da janye dakarun kasarsa daga Mali, idan akwai karuwar barazanar masu tsattsauran ra'ayi biyo bayan juyin mulki.

https://p.dw.com/p/3uBdJ
Symbolbild Mali Islamistischer Terrorismus
Hoto: Baba Ahmed/AP/dpa/picture alliance

A farkon wannan makon ne dai aka tilasta wa shugaban kasar Bah Ndaw da Framinista Moctar Ouane yin murabus daga mukamansu, bayan tsaresu da aka yi biyo bayan kifar da mulkin da mataimakin shugaban kasar ya jagoranta.

Macron ya ce ya ga alamun hakan a mali, kuma idan barazanar ta karu, ko shakka babu zai janye dakarunsa zuwa gida.