1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faragabar kiristoci 'yan koptik a Masar

Dennis StuteAugust 21, 2013

Kiristoci mabiya darikar Koptik na nuna damuwa game da tashen-tashen hankula da ke ritsawa da wurarensu na ibada da dukiyoyinsu tun bayan da aka hambarar da Mohamed Morsi daga karagar mulkin Masar.

https://p.dw.com/p/19UKQ
Hoto: Reuters

Da ma dai kiristoci mabiya darikar koptik sun saba cin karo da matsaloli a rayuwarsu ta yau da kullum a kasar Masar. Sai dai kuma lamarin ya ci-gaba da tabarbarewa bayan da sojoji suka hambarar da zababben shugaba Mohamed Morsi daga karagar mulki a ranar 3 ga watan Yuli. A hakikanin gaskiya ma dai murkushe daruruwan magoya bayan Kungiyar 'Yan Uwa Musulmi da aka yi ya zame wa 'yan koptik alakakai. A cewar Ishak Ibrahim na kungiyar Kara hakkib bil Adama ta EIPR a ranar 14 ga watan Agusta kadai hare-hare daya bayan daya har guda 44 aka kaddamar a wuraren ibada na 'yan Koptic, inda aka lalata musu wurarensu na ibada da ma dukiyoyi tare da kuma da jikata wasu daga cikinsu. Wannan jami'in cewa ya yi hare-haren ba sa rasa nasaba da zaman doya da manjan da tun fil-azam ake fuskanta tsakanin 'yan Koptic da kuma 'ya'yan Kungiyar 'Yan Uwa Musulmi.

Koptische Kathedrale St. Mark in Kairo
cocunan Koptik da dama aka rusa a MasarHoto: DW/A. Hamdy

"Mun lura da yadda shugabannin Kungiyar 'Yan Uwa Musulmi suka tunzura magoya bayansu ga far ma kiristoci mabiya darikar koptik. Sun nuna musu cewar 'yan koptik sun goyi bayan sojoji lokacin da suka hambarar da gwamnatin masu rajin Islama."

Takun saka tsakanin musulmi da 'yan koptik

Shugabannin Kungiyar 'Yan Uwa Musulmi sun zargi 'yan koptik da rashin kaunar duk wani abin da ke da alaka da shari'ar musulunci a Masar. Ko da a shafinsu na sa da zumunci na facebook, sai dai suka bayyana cewa shugaban darikar koptik ne ya ke ruruta wutan rikicin da ke ci a yanzu, a inda ya ke daure ma wadanda suke kone-konen masallatai gindi.

Sai dai kuma a wasu jawaban da suka yi a baya 'yan Kungiyar 'yan uwa musulmi kansu suka amince cewa masu ra'ayin addini suka kai wa 'yan koptik hare-hare. Ko da a farkon watan nan na Agusta da muke ciki, sai da a ka fuskanci rikici a garin Bani Ahmed a lardin charkia tsakanin kirista da ke kin jinin Morsi da kuma musulmin da ke goyon bayan hambararen shugaban. Ishak Ibrahim na kunfgiyar EIPR ya yi bayani game da zahirin abin da ya faru.

"Daruruwan musulmi sun kai hare-hare a kauyuka da dama inda suka banka wa gidajen kiristoci da kuma majami'u wuta. Su kiristocin sun yi iya kokarainsu wajen kare dukiyoyinsu, amma daga bisani gidaje 43 ne suka kone."

Doka ba ta kare tsirarun 'yan koptik a Masar

'Yan sanda sun yi tattaki i zuwa garuruwan da aka kai hare-haren amma kuma a makare. A mafi yawancin lokuta, bangarorin biyu wato wa kiristoci mabiya darikar koptik da kuma musulmi na zama kan teburin tattaunawa don magance sabanin da ke tsakaninsu. Su ma dai hukomomin Masar sun yi na'am da ire-iren wadannan matakai da ake dauka domin samar da zaman lafiya tsakanin mabiya addinai daban daban. Amma kuma inda gizo ke sake shi ne ba a hukunta wadanda suke da hannu wajen tayar da rikicin da kuma wadanda suka aikata ta'asa. Maimakon haka ma dai a cewar Ishak Ibrahim sansanta rikicin ake yi cikin ruwan sanyi.

Koptische Christen in Ägypten
'yan Koptiki sun shiga an dama da su a zanga-zangaHoto: picture-alliance/Arved Gintenreiter

"Kiristoci na janye karar da suka shigar gaban 'yan sanda ba tare da an biyasu diyya ba. Sai dai kuma ko da bangarorin biyu sun sake kai ga sake yin fito na fito suna kauce wa kona wuraren ibadan junansu."

Babu dai wasu dokoki da aka dauka karkashin zamanin mulkin Mubarak da kuma Morsi domin kare tsirarun kiristoci mabiya darikar koptik a Masar. Saboda haka ne me wasu kungiyoyin da suka himmatu wajen kare hakkin bani Adama ke ganin cewa da kamar wuya a kawo karshen musgana wa 'yan koptik a Masar cikin wani takaitacen lokaci.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Mohammad Nasiru Awal