1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An fara yakin neman zaben shugaban kasar Senegal

Robert Adé Mouhamadou Awal Balarabe/SB/MA
March 11, 2024

Yakin neman zaben shugaban kasa a Sengal na ci gaba da gudana a cikin yanayi na azumin watan Ramadana da azumin Kiristoci, lamarin da ya zama kalubale ga 'yan takara a wannan kasa da ke yankin yammacin Afirka.

https://p.dw.com/p/4dOix
Yakin neman zabe a Senegal
Yakin neman zabe a SenegalHoto: SEYLLOU/AFP

A kasar Senegal, yakin neman zaben shugaban kasa na ci gaba da gudana a cikin yanayi na azumin watan Ramadana da azumin Kiristoci, lamarin da ya zama kalubale ga 'yan takara. A  ranar 24 ga watan Maris ne zaben zai gudana, amma a birnin Dakar 'yan takara na amfani da dabaru wajen jan hankali masu kada kuri'a, a wannan kasa mai rinjayen Musulmi. Ko yaya 'yan Senegal ke hada yakin neman zabe da azumin Kirista da Musulmi?

Karin Bayani: Senegal: Sabuwar ranar zabe daga kotu

Yakin neman zabe a Senegal
Yakin neman zabe a SenegalHoto: SEYLLOU/AFP

Sannu a hankali ne dai yakin neman zaben shugabancin kasar Senegal ya fara a ranar Asabar, amma a yanzu  tarurruka sun fara kankama musamman a Dakar babban birni, inda ake samun ayarin 'yan takara da ke kewaya sako da lungu domin tallata manufofinsu. A bangaren gamayyar FC 25 wacce ta hada 'yan takarar shugabancin kasar Senegal 16, an samu kwanciyar hankali da kwarin gwiwar samun nasara makonni biyu kafin zaben na 24 ga watan Maris.

Fatou Bintou Sarr, ita ce ke kula da reshen mata a gundumar Pikine Nord na yakin neman zaben shugaban kasa na Bassirou Diomaye Faye da ke da kusanci da madugun hamayya Ousmane Sonko, kuma ta ce ba abin mamaki ba ne idan gwaninsu ya lashe zaben tun a zagayen farko saboda shirin da suka yi.

A karon farko cikin tarihin siyasar kasar Senegal, ana gudanar da yakin neman zaben shugaban kasa a tsakiyar watan Azumi, watan Ramadana ga Musulmi da kuma ta Ista ga Kirista. Hasali ma, yana zama babban kalubale ga 'yan takara da ke azumi saboda kuzari da suke bukata. Moctar Ndiaye da ke zama masanin addinin MusuIunci kuma limamin a babban masallacin Liberté 6 da ke birnin Dakar, ya ce ya kamata duk Musulmi mumini ya guje wa wasu munanan hali a wannan yanayi na hada yakin neman zabe da azumi da ke zama ibada.

Yakin neman zabe a Senegal
Yakin neman zabe a SenegalHoto: SEYLLOU/AFP

Galibin 'yan takarar 19 imma a bangaren shugaban kasa ko 'yan adawa ko ma kungiyoyin farar hula ne sun kaddamar da yakin neman zabensu a yankin Dakar da kewayensa, inda wasunsu suka yi amfani da wannan dama wajen gabatar da abubuwan ci-gaba da suke wa al'umma alkawari. Sai dai kwararre kan harkokin zabe, El Hadji Saidou Nourou Dia, ya yi gargadin cewar matsalar da za a iya fuskanta, ita ce ta shawo kan mutane domin su je su kada kuri'a a wannan lokacin azumin Ramadana.

An riga an fara maka tutocin jam'iyyu da fastoci da ke dauke da hotunan wasu 'yan takara a manyan tituna da wuraren masu muhimmanci da ke cikin garin Dakar. Akasarin 'yan takara 19 na Senegal na halartar zagayen farko na zaben 24 ga watan Maris 2024 a karon farko, in banda Idrissa Seck wanda wannan shi ne zabensa na biyu baya ga zaben shugaban kasa na 2019.