1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus na duba yiwuwar dawo da wasu matakan yaki da Corona

Abdoulaye Mamane Amadou
September 16, 2022

Majalisar zartawa a Jamus na nazarin soma amfani da sabbin dokokin yaki da annobar Corona da majalisar dokoki ta Bundestag ta samar

https://p.dw.com/p/4GzRO
Deutschland | Olaf Scholz zum Tod von Königin Elizabeth II.
Hoto: Bernd von Jutrczenka/dpa/picture alliance

Daga cikin sabbin dokokin da majalisar zartarwar Jamus ke shirin dubawa su fara aiki a farkon watan Oktoba na 2022 sun hada da tilasta saka takunkumin fuska a cikin jiragen kasa idan ana tafiya mai nisa da asibitoci, sai dai sauran jihohi na iya amfani da matakin don tilasta amfani da takunkumi a gidajen cin abinci, kana ana shirin dage amfani da dokar saka takunkumin fuska ga masu tafiye-tafuiye a jirgin sama.

Jamus ta kuma bayyana anniyarta na kin sake komawa a duk wasu matakan dokar kulle a wuraren kasuwanci da makarantu a cewar ma'aikatar kiwon lafiya ta kasa.