Fa'idar shayar da jariri nonon uwa zalla
August 2, 2022Shi dai shayar da jariri nonon uwa zalla kamar yadda hukumar lafiya ta duniya WHO ta nunar idan an haifi jariri za a rika bashi nonon uwa ne kawai har na tsawon watanni shidda, shawarwarin da tuni iyayen dake shayarwa suka fara ganin ci gaban sa.
Dr Amadu Abdu Mamadu shugaban sashen kula da lafiyar uwa da jarirai a babban asibitin haihuwa na Damagaram yace tsarin yana da matukar fa'ida ga lafiyar jariri, hasali ma kuma yana kara dankon soyayya tsakanin uwa da jaririnta.
A yayin da wasu matan ke bada nonon tsantsa ga jariransu, wasu iyayen kuma na bijire wa hakan saboda wasu dalilai na kashin kansu.
Dr Amadu Abdu Mamadu ya kara da cewa bai wa jariri nonon uwa zalla yana taimakawa wajen rage jinkirin girma ga jariri da 40% ko rage karancin jini da 50% ga mata masu juna biyu.