Fafutukar warware rikicin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya | Labarai | DW | 20.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fafutukar warware rikicin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Shugabannin da gwamnatoci na ƙasashen yankin tsakiyar nahiyar Afirka na ƙungiyar za su gudanar da wani taro a Cadi domin samar da mafita ga rikicin ƙasar.

Taron wanda shugaban ƙungiyar ne da ke ci yanzu Idriss Deby ya kira shi, zai tattauna matsalar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya,wacce ke fama da tashin hankali na ƙabilanci da kuma hare-hare da fyaɗe da sojoji ke kai wa akan farar hula.

Wannan taro dai shi ne na biyar da ƙungiyar ta ke yi a kan Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya,tun bayan juyin mulkin da Michel Djotodia ya yi wa shugaba Francois Bozize,a cikin watan Maris da ya wuce a ƙarkashin jagorancin ƙungiyar 'yan tawayen ta SELEKA. A cikin watan jiya shugaba Francois Hollande na Faransa, ya ce zai ƙara yawan sojojinsa a Jamhuriyar Afirka ta Tasakiyar,domin kawo ɗauki ga rundunar tsaro ta ƙasashen Afirka MISCA don samar da zaman lafiya.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane.
Edita : Zainab Mohammed Abubakar