1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaki da ta'addanci a yankin Sahel

Ramatu Garba Baba
May 13, 2018

Kasashe biyar na Afirka sun shirya tura wata rundunar yaki da ta'addanci ta hadin gwiwa a yankin Sahel, rundunar za ta yi aiki tare da ta Majalisar Dinkin Duniya .

https://p.dw.com/p/2xeYi
USA Soldat Militärausbilder in Afrika
Hoto: dapd

Ministan harkokin tsaro na Nijar Kalla Moutari ne ya sanar da hakan bayan wani zama da suka yi da takwarorinsa na sauran kasashen a birnin Ouagadougou na kasar Burkina Faso a wannan Lahadin. Rundunar da ta kunshi dakaru dubu biyar za ta yi aiki hannu da hannu da sojin Faransa da kuma na Majalisar Dinkin Duniya da aka jibge a yankin don tunkara da kuma ganin bayan kungiyoyi da ke wa zaman lafiya a yankin barazana.