Fafutukar fadikar da matasa a Abidjan | NRS-Import | DW | 03.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

NRS-Import

Fafutukar fadikar da matasa a Abidjan

DW tare da tallafin ofishin ministan harkokin waje na Jamus sun shirya wata muhawara ta benar jama'a a birnin Abidjan na Cote d'Ivoire da nufin wayar da kan matasa da ke yin kaura ba bisa ka'ida ba zuwa Turai.

Wasu daga cikin 'yan cirani biyu da suka yi kaura, suka dawo gida

Wasu daga cikin 'yan cirani biyu da suka yi kaura, suka dawo gida

Muhawarar mai taken yin kaura ba bisa kaida ba, ta biyo bayan wadda DW ta shirya a biranen Bamako na Mali da kuma Dakar na Senegal da nufin wayar da kan matasa da ke yin kasadar tsallakawa ta hanyar teku zuwa nahiyar Turai cikin jiragen ruwa marasa inganci. An gudunar da wannan muhawara ce a benar jama'a wacce ta samu halartar kwararrun da aka tattauna da su wadanda suka hada da  jami'an gwamnati da wakilai na kungiyoyin farar hula  da mayan mallamai na jami'a da ma wasu daga cikin 'yan cirani da suka ba da shaidu na irin matsalolin da suka ci karo da su a kan hanyar su ta zuwa Turai sannan kuma  da wasau darurruwan jama'ar 

'Yan kallo a muhawarar da Dw ta shirya a benar jama'a a Abidjan

'Yan kallo a muhawarar da Dw ta shirya a benar jama'a a Abidjan

da suka je kallon muhawara a cibiyar raya al'adu ta Jamus watau Goethe da ke a birnin Abidjan a ranar juma'a da ta wuce da yamma. Dukkanin kwararrun da aka tattauna da su, sun yi itipakin cewar matsalar ta yin kaura ba bisa ka'ida ba abu ne da ke ciwo jama'a tuwo a kwarya a yanzu, sakamakon yadda ake samun dimbin matasa da suke rasa rayukan su a lokacin da suke yin kokarin tsallakawa zuwa nahiyar Turai ta tekun cikin jiragen ruwa marasa inganci, wannan ma shi ne dalilin da ya sa DW ke shirya irin wannan muhawara ta benar jama'a domin kawo na ta kokarin na magance matsalar.

 

Sauti da bidiyo akan labarin