Fafatawar gasar Olympic a Koriya ta Kudu | Zamantakewa | DW | 13.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Fafatawar gasar Olympic a Koriya ta Kudu

A karshen mako Redmond Gerad dan shekaru 17 da haihuwa, ya zama mafi karancin shekaru da ya samu lamban zinare lokacin gasar gudu na zamani da nuna bajinta a kan kankara.

Kasashen duniya na ci gaba da karawa tsakani a gasar Olympic na lokacin hunturu da birnin PyeongChang na Koriya ta Kudu ya dauki nauyi, tuni aka lashe lambobin yabo da dama a gasar kawo yanzu.

Kasashe:                    Zinare   Azurfa   Tagulla  Jimla

Jamus                            3            0             1          4

Holland                          2            2             1          5

Amerika                         2            1             1          4

Norway                          1            4             3          8

Kanada                          1            4             1          6

A wannan gasa na birnin PyeongChang wakilan da suka fito daga kasar Koriya ta Arewa na zama wadanda suka dauki hankali bisa dalilan siyasa, da zaman-tankiya da aka dade ana samu tsakanin kasar da Koriya ta Kudu da kuma Amirka. A dayan hannun kuma manyan jami'an gwamnatin Koriya ta Arewa da suka halarci gasar sun samu kekkyawar tarba.