Fafaroma ya ja hankali a kan matasa | Labarai | DW | 22.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fafaroma ya ja hankali a kan matasa

Fafaroma Francis da ya kai ziyarar aiki Brazil ya yi gargadi game da zaman kashe wando da matasa ke fama da shi a duniya, inda ya ce shi ne ke jefasu cikin wani mummunan hali.

Paparoma Francis ya yi kira da a samar wa matasa da guraben aiki matikar ana so a cetosu daga mawuyacin hali da suka samun kansu a ciki a halin yanzu. A lokacin da ya ke jawabi a cikin jirgin da ke kaishi Brazil inda zai shafe mako guda, fafaroma ya nunar da cewa magance zaman kashe wando ne zai ba wa matasa damar rike kansu da kansu da ma dai kimar kasashensu. Da ma dai a watan da ya gabata duban matasan Brazil sun gudanar da zanga-zanga domin yin Allah wadarai da matsalar rashin aikin yi da ke ci musu tuwo a kwarya.

Wannan dai shi ne karon farko da fafaroma Francis ya tashi daga birnin Rome na Italiya zuwa wata kasa ta waje, tun bayan darewarsa kan kujerar shugabancin darikar Romankatolika a watan Maris da ya gabata. Makasudin wannan ziyarar dai shi ne halartar bukuwar ranar matasa ta duniya da za su gudana a birnin Rio de Janairo. Agendar ta Fafaroma Francis wanda dan asalin kasar Argentina ne, ta tanadi ganawa da 'yan Brazil da ke rayuwa hannu baka hannu kwarya a wata unguwa ta ya ku bayi, da kuma kai wa marasa lafiya ziyara a wani asbiti

Kimanin mutane miliyan daya da dubu 500 ake sa ran za su halarci wadannan bukukuwa na matasa da kasar Brazil ke daukan bakwancinsu.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu