Fafaroma ya ce a samar da ′yancin addini | Labarai | DW | 26.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fafaroma ya ce a samar da 'yancin addini

Shugaban darikar Katolika ta duniya Fafaroma Francis ya bukaci da a samar da kariya da kuma 'yancin yin addini ga ma'abota addinai daban-daban a duniya.

Fafaroma ya yi wannan kiran ne yayin bikin ranar bada kyaututtuka a ci gaba da shagulgulan bikin Kirsimeti da ake yi a fadin duniya baki daya. Fafaroma ya kuma yi amfani da wannan dama wajen girmama Kiristoci dake cikin halin tasku a fadin duniya, tare da yi musu addu'o'i. Rahotanni sun nunar da cewa Fafaroma Francis ya yi addu'oi na musamman ga Kiristoci tsiraru da ke yankin Gabas ta Tsakiya.

Tun da fari dai Fafaroman ya tattauna ta wayar tarho da Kiristocin da 'yan ta'addan IS suka tilastawa kauracewa gidajensu wadanda ke sansanin 'yan gudun hijira na Ankawa da ke tsakiyar yankin Kurdistan na kasar Iraqi tare da yi musu kalamai na kwantar da hankali.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mohamadou Awal Balarabe