1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi kira ga jagororin addinin Kirista

Zulaiha Abubakar
January 3, 2019

Shugaban Kiristoci mabiya darikar Katolika Fafaroma Francis ya ja hankalin Jagororin addinin a Kasar Amirka da su hada kai a yaki da cin zarafi a guraren ibada.

https://p.dw.com/p/3B0lY
Vatikanstaat Weihnachten 2018 | Urbi et orbi, Papst Franziskus
Hoto: Reuters/M. Rossi

Yanzu haka dai jagororin Cocin Amirkan na gudanar da wani taro don nemo  hanyoyin kawo karshen rikici a tsakaninsu,Fafaroma ya jaddada bukatar fito da sabbin tsare-tsare don magance cin zarafin mata da kannan yara a majami'u a cikin wata budaddiyar wasika daya aike gurin taron bayan ya gargadi shugabannin addinin da aka samu da laifi su guji zargin juna.