1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fafaroma na taro kan lalata da yara a coci

Zulaiha Abubakar
February 21, 2019

Shugaban darikar Katolika ta duniya Fafaroma Francis zai bude baban taron kwanaki hudu a wannan Alhamis a birnin Vatican don yin nazari kan lalata da yara da aka samu wasu limaman cocin katolika da aikatawa.

https://p.dw.com/p/3Dlor
Papst Franziskus in Vatikan
Hoto: Getty Images/AFP/A. Solaro

Ana sa ran sama  da jagororin Cocin Katolila 200 ne za su halarci taron don nemo mafita game da yawaitar cin zarafin kananan yara a guraren ibadar da ke kasashen Amirka da Chile. Gabanin taron dai, tawagar wasu masu wa'azi daga gamayyar kungiyar Cocin Katolika da yawansu ya kai 114 za su yi ganawar sirri da wadanda suka fuskanci cin zarafi a majami'u da guraren ibadar Kiristocin.

Daga cikin batutuwan da babban taron zai tabo har da shirin wayar da kan jama'a kan yawaitar rikici a kasashen Afirka da Gabas ta Tsakiya.