Fafaroma ya tausayawa yaran da aka ci zarafi a Coci
August 17, 2018Talla
Binciken ya hada da shaida akan yadda limaman Cocin dake cin zarafin yara kanana ke samun garkuwa daga manyan jagororin Coci da kuma yadda ake saurin canza wa masu wannan ta'annati gurin aiki ba tare da an sanar da mabiyan su dalili ba,a jiya Alhamis tawagar wasu limaman darikar Katolika a Amirka suka gayyato fadar Vatikan yayin da suke gudanar da babban taron su don ganin irin rawar da fadar zata taka yayin binciken Pastor McCarrick wanda ake zargi da lalata yara kanana a tsangayar horar da limaman Addinin Kirista.
A baya dai an jima ana zargin wasu limaman manyan majami'u da fakewa da addini suna lalata da mata da kananan yara.