Fafaroma Francis ya yi kiran da a zauna lafiya
April 28, 2017Talla
Ziyarar wacce ta kwanaki biyu ce na zuwa ne daf da lokacin da kasar take cikin wani hali na dokar ta baci, bayan tagwayen hare- hare da Kungiyar IS ta kai a kan Kiristoci Kibdawa a farkon wannan wata wanda a ciki mutane 45 suka mutu. Yanzu haka hukumomi a kasar ta Masar sun karfafa tsaro a ko'ina domin kiyaye afkuwar wasu hare-hare.