1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ci gaba da shagulgulan bikin Kirsimeti

Zulaiha Abubakar MNA
December 25, 2018

Shugaban mabiya darikar Katolika ya baiyana rashin wadatar zuci a matsayin ginshikin da ya jefa al'umma cikin rudani yayin da yake jawabi a fadar Vatican daidai lokacin da aka fara bikin Kirsimeti.

https://p.dw.com/p/3Abko
Vatikanstaat Weihnachten 2018 | Urbi et orbi, Papst Franziskus
Hoto: Reuters/M. Rossi

Jagoran mai shekaru 82 ya koka game da yadda mutane kalilan suke rayuwa cikin daula yayin da mafi yawa ke samun abin da za su ci da kyar.

Fafaroman ya yi suka da yadda almubazzaranci ya yi yawa a duniya, kana ya yi kira da a taimaka wa masu karamin karfi a cikin al'umma. 

Mabiya addinin Kirista na gudanar da bukukuwan Kirsimeti a kasashe dabam-dabam a wannan Talatar, daidai lokacin da mabiya addinin ke kokawa game da yadda ake samun karuwar hare-hare a guraren ibadu.