Fafaroma Francis ya isa Bolivia | Labarai | DW | 09.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fafaroma Francis ya isa Bolivia

Dubun dubatar al'ummar Bolivia ne suka kwana a tituna dan dakon Fafaroma Francis saboda neman tabaraki a wannan ziyara mai dinbin tarihi.

Papst Franziskus in Bolivien

Fafaroma Francis da masu tarbarsa a Bolivia

A ranar Alhamis din nan ce Fafaroma Francis ya isa Bolivia a ziyarar ibada da yake yi a Kudancin Amirka .

A lokacin wannan ziyarar zai yi wani zaman addu'a da kungiyoyin al'umma 'yan asalin kasar da ma wasu kungiyoyi da ke aikin tallafi ga al'umma marasa galihu.

Fafaroma Francis ya sami gagarimar tarba daga shugabanni da manyan fada-fada na coci.

Dubun dubatar al'ummar Bolivia ne suka kwana a tituna dan dakon Fafaroma saboda neman tabaraki kamar yadda wannan mata ke cewa:

"Muna neman tabaraki daga fafaroma Francis dan haka nazo nan da 'ya ta 'yar watanni hudu da 'yan uwanta mun tsaya a wannan titi mun kwana dan tsamanin ko zamu yi ido biyu da shi mu samu tabarraki".