Fafaroma Francis ya bayyana fargabansa | Labarai | DW | 15.11.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fafaroma Francis ya bayyana fargabansa

Fafaroma Francis ya yi kiran da a yi hattara a game da irin kalaman da 'yan siyasa ke yadawa a yanzu wanda ya ce suna yi masa tuni da irin na 'yan mulkin Nazi.

Fafaroma Francis ya ce kalaman na 'yan siyasa sun yi kama da irn jawabin da Hitler ya rika yi na nuna kyama ga Yahudawa da kuma 'yan luwadi da madigo. Fafaroma wanda ya bayyana haka a loacin wata ganawa da jami'an wata kungiyar ta kare hakin bil Adama na kasa da kasa ya ce ya zama waji a rika saka ido ga abin da ka iya zama fitina ga duniya. Fafaroma Francis ya yi kashedi ga irin tsongoma da ake kokarin sake dawo da ita a kan Yahudawa.