1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fafaroma Francis ya amince da ajiye aikin Cardinal Donald

Zulaiha Abubakar
October 12, 2018

Rahotanni daga fadar Vatican sun bayyana cewar shugaban Kiristoci mabiya darikar Katolika Fafaroma Francis ya amince ta ajiye aikin Archbishop din birnin Washington Cardinal Donald Wuerl .

https://p.dw.com/p/36Sqs
Mögliche Papstnachfolger - Donald Wuerl
Hoto: Getty Images

Tun da farko Fafaroma Francis ya roki tsohon Archbishop din na  Washinton da ya ci gaba da rikon kwarya har zuwa lokacin da za a samu wanda zai maye gurbin sa lamarin da ya  tabbatar da irin kau da kan da Fafaroma yake yi a al'amuran wasu jagororin Addinin.Kafin saukarsa daga Mukami Cardinal din ya rubuta wata budaddiyar wasika wacce kuma ya bukaci a karantawa magoya bayansa a fili inda ya roki gafarar duk wadanda aka ci zarafi a guraren ibadu tare da rokon jama'a  yafe masa bisa yadda ake masa kallon mai kare limaman Cocin da ke cin zarafin mata da yara kanana.