Fafaroma: Fahimta ce warakar rikicin addini | Labarai | DW | 31.03.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fafaroma: Fahimta ce warakar rikicin addini

Hanyar tattaunawa ita ce za ta sanya soyayya tsakanin mabiya addinai dabam-dabam, a kawar da kin juna a cewar Fafaroma Francis.

Fafaroma Francis a wannan rana ta Lahadi ya yi kira na ganin samun kyakkyawar danganta ta hanyar tattaunawa tsakanin Musulmai da Kirista. Ya ce tattaunawar ita ce hanya da za ta sanya mabiya addinin da ba su da rinjaye a wata kasa su ji kamar su ma bangare ne na al'ummar wannan kasa, matakin da zai taimaka wajen yaki da tsattsauran kishin addini.

A rana ta biyu kuma ta karshe ta ziyarar ta Fafaroma a Maroko, ya gana da manyan malamai da mabiya addinin Kirista karkashin darikar ta Katolika inda ya fada masu cewa duk da cewa adadinsu ba shi da yawa a kasar hakan ba yana nufin bi ko ta halin kaka wajen ganin sun ja hankalin mutane su shiga addininsu ba, amma dama ce ta tattauanawa da aiyuka na alheri tsakanin su da wadanda ba Kirista ba. A cewar Fafaroma hakan zai kawo fahimta da kawar da kyama ko jin haushin na juna.