Fadakar da Limamai kan tsaurin ra′ayin adini | Zamantakewa | DW | 15.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Fadakar da Limamai kan tsaurin ra'ayin adini

Cibiyar horas da Limamai ta sarkin Maroko Muhammad Na 6, ta shirya taron bita ga Limaman yankunan da ke fama da ta'addanci a kasashen Afirka.

Afrikaner in Brasilien Senegalesische Migranten

Matasa 'yan kasar Senegal su na karatun Alkur'ani

Manufar shirya wannan bita dai ga limaman masallatai da masu wa'azi maza da mata da suka fito daga kasashen Afirkan da ke fama da kungiyoyin yan ta'adda shi ne, koya wa mahallartan bitar hanyoyin yada matsakaicin ra'ayin Islama da mutunta ra'ayoyi mabanbanta, gami da koya wa limaman dubarun da za su bi don dawo da fandararru kan turba, a ta bakin shugaban cibiyar da aka bude ta bara, Abdussalam Al-Araj

"Ginshikin kafa wannan cibiya shi ne, koyar da matsakaicin ra'ayin Islama da tunkarar batanci da ake wa Musulunci daga su kansu musulmin da suka yi masa mummunar fahimmata ko kuma wadanda ke neman yi masa batanci da gangan amanar cewa, ba abin da zai iya magance wuce gona da iri da ta'addanci, kamar koya wa mutune mahimmancin dukufa kan ibada da gyaran hali, da kuma koyar da su sahihin addininsu. Sheik Mazin Fathy, daya daga cikin maluman da suka gabatar da kasida a yayin bitar, ya bayyana tasirin da gyaruwar limamai da masu wa'azi yake dashi wajen gyaruwar al'umma:

Äthiopien Muslime Opferfest Eid Al Adha

Musulmai na sallah a kasar Habasha

"Ma'aiki S.A.W yayi kira garemu da mu zama tsinsiya madaurin ki daya, mu kuma kauce wa duk abin da zai kawo rarrabuwar kanu tsakanin al'umma. Maluma kuma su ne magadan Annabawa da ya wajaba da su dinga tabbatar ana aiki da wannan sako. Muddin muka hade wuri guda, to yan ta'adda da masu matsanancin ra'ayi ba za su sami damar yin kutse cikinmu ba."

Batun mutunta ra'ayoyi mabanbanta da ke zama jigo wajen samar da zaman tare cikin lumana tsakanin bangarori masu sabani ko banbancin fahimta, batu ne da Sheik Ahmad Abul fatah Hasan, wani limami daga kasar Chadi ya ce sun koya a yayin bitar da aka yi.

Großmoschee von Khartum Archiv 2008

Wani babban Masallaci a birnin Khartum na Sudan

"Akwai wani darasi mai suna "Hanyoyin ganawa da jama'a" wanda ya koya mana irin rawar da limamai za su taka, ba wajen koyar da ibada kadai ba, har ma da dabarun sasanta tsakanin al'umma."

Kasancewar kungiyoyin yan ta'adda su na amfani da mata a matsayin masu kai hare haren kunar bakin wake ko wadanda suke garkuwa da su ko matan dole, taron bitar ya fayyace yadda za'a iya dawo da irin wadannan mata cikin dangi, bayan an 'yanto su daga hanun yan ta'addar, a ta bakin Hasanatu Niyana, wata mai wa'azi daga kasar Guinea.

"Za mu dinga koya wa irin wadannan mutane yafar juna ne, da kokarin manta baya, bayan an koyi darasi, don tunkarar gaba. Domin idan har da gaske mu musulmai ne, to dole ne kar musuluncinmu ya takaita kan sunaye da tufafi, wajibi ne aga musuluncin a halaye da ayyukanmu."