An koma gwabza yaki a arewacin Kamaru
December 10, 2019Talla
Kungiyoyin da ke yin aikin agaji a yankin sun ce farar hula sun fada cikin tarkon sasan biyu masu gaba da juna, lamarin ya kara dagulewa ne bayan da taron kasa da shugaba Paul Biya ya kira don tattaunawa ya gaza cimma wani sulhu tsakanin gwamatin da 'yan aware. Kungiyar agaji ta Human Rights Watch ta ce daga watan Yuli zuwa yau kusan farar hula 130 a ka kashe a tashin hankalin da a shekaru biyu sama da mutane dubu 700 suka fice daga matsugunansu.