1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana neman mafita ga gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar

November 15, 2022

Birnin Goma da ke kasancewa babban birnin arewacin Lardin Kivu na ci gaba da fuskantar barazana daga 'yan tawayen kungiyar M23, abin da ke hargitsa lamura a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango.

https://p.dw.com/p/4JXVG
Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango I Matasa masu shiga soja
Matasa masu shiga soja a Jamhuriyar Dimukuradiyyar KwangoHoto: Zanem Nety Zaidi/DW

A Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, birnin Goma da ke kasancewa babban birnin arewacin Lardin Kivu na ci gaba da fuskantar barazana daga 'yan tawayen kungiyar M23. Masu fafafutuka da sauran kungiyoyin fararen hula a kasar na zargin gwamnatin kasar da nuna halin rashin kula wajen magance rikicin da kasar ta fada, inda suke ganin kasar na dogaro ne da dakarun ketare.

Karin Bayani:Rikici a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango

Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, masu zanga-zanga a garin Goma
Masu zanga-zanga a Jamhuriyar Dimukuradiyyar KwangoHoto: Michael Lunanga/AFP

An kwashe tsawon kwanaki ana tafka kazamin fada a yankin Kibumba, kilo mita 23 da birnin Goma da ke gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango, sai dai 'yan kasar na zargin gwamnatin da yin rikon sakainar kashi wajen daukar matakan da suka dace don kawo karshen ayyukan 'yan tawayen M23 a kasar kamar yadda guda daga cikin shugabannin kungiyoyin fararen hula a kasar  Constantin Werabe ya bayyanawa DW.

Kawo yanzu dai, shugabannin kasashen gabashin Afirka sun shirya gudanar da tattaunawar zaman lafiya kan rikicin na gabashin Kwango. Kungiyar ta ce ta shirya gudanar da tattaunawar a ranar 21 ga watan Nuwanban nan da muke ciki a Nairobi babban birnin kasar Kenya. Tun a karshen makon da ya gabata ne dai dakarun kasar Kenya suka isa kasar ta Kwango don wanzar da zaman lafiya a kasar. Tawagar ta dakaru kimanin 100 na Kenyar za su hada gwiwa da sojojin Kwangon wajen ci gaba da yakar kungiyoyin 'yan tawayen kasar. Sai dai a cewar Farfesa Daddy Saleh, masanin siyasa a kasar ya ce dakarun na kenya ba wani tasiri da za su yi kamar yadda aka gani cikin shekaru da dakarun wanzar zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya suka yi a kasar

Sojonin Kenya da aka tura Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango
Sojojin KEnya masu zuwa Jamhuriyar Dimukuradiyyar KwangoHoto: Brian Inganga/AP/picture alliance

Sai dai mazauna birnin na Goma kamar su Kasereka Munyamfura na maraba da dakarun na Kenya tare da fatan za su iya kawo karshen rikicin na gabashin Kwangon.

Dangantaka dai ta yi tsami tsakanin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da makwafciyarta Ruwanda, tun bayan da gwamnatin Kinshasa ta zargi Ruwanda da goyon bayan 'yan tawayen, sai dai gwamnatin Kigali ta musanta zargin.