Fada ya rincabe a Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya | Labarai | DW | 10.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fada ya rincabe a Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya

Magoya bayan tsiohon shugaba Bozize, sun karbi iko da wasu kauyuka daga dakarun gwamnatin wucin gadi.

Majiyoyin soji a jamhuriyyar Afirka Ta Tsakiya, sun sanar da cewar, a wannan Talatar ce, magoya bayan hambararren shugaban kasar, Francois Bozize, suka yi nasarar karbe iko a wasu kauyukan da ke kusa da Bossangoa, bayan wani fadan da ya janyo mutuwar a kalla mutane 60. Wani jam'in sojin da ya bukaci a sakaya sunansa, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewar, wasu mayakan da ke ikirarin yi wa tsohon shugaba Bozize aiki, sun kwace ragamar mulki a kauyukan da ke kewaye da garin Bossangoa, dake yammacin kasar, ko da shike kuma jami'an tsaron gwamnati ne ke da iko da garin.

Levy Yakete, kakakin tsohon shugaba Bozize da 'yan tawayen Seleka suka kifar da gwamnatinsa a ranar 24 ga watan Maris, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa cewar, dakarun da ke goyon bayan hambararren shugaban ne, wadanda ke zama wani bangare na rundunar FACA, su ne ke fafatawar. Ya ce dakarun na daukar matakin ne domin mayar da martani ga irin ta'asar da 'yan tawayen Seleka ke tafkawa.

Bozize dai ya mulki kasar na tsawon shekaru 10, bayan darewa kujerar mulki ta hanyar juyin mulkin soji a shekara ta 2003, kuma sau biyu ana sake zabensa zuwa ofis.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe