Fada tsakanin magoya baya da masu adawa da Assad ya jawo rasa rayuka
March 21, 2014Talla
A kalla mutane bakwai ne aka bada labarin rasuwarsu a wannan Juma'ar (21.03.2014) a birnin Tripoli da ke arewacin kasar Lebanon, bayan da fada ya barke tsakanin masu adawa da shugaban Siriya Bashar al-Assad da kuma magoya bayansa.
Masu aiko da rahotanni suka ce daga cikin wadanda suka rasa ransu har da wani dattijo, yayin da kimanin mutane 11 suka jikkata.
Dama dai an jima ana takun saka tsakanin mabiya tafarkin Sunnah na wannan gari na Tripoli da 'yan Alawiyya wanda ke goyon bayan Shugaba Assad, wanda yanzu haka ya ke fuskantar tada kayar baya a kasarsa daga masu rajin ganin ya kau daga mulki.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Saleh Umar Saleh