EU za ta sake tattaunawa kan Girka | Labarai | DW | 20.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

EU za ta sake tattaunawa kan Girka

Ministocin kuɗi na Ƙungiyar Tarrayar Turai za su sake tattaunawa a karo na uku a Brussels a kan batun Girka.

Tsipras Alexis Griechenland Parlament Athen Ministerpräsident Syriza

Tsipras Alexis firaministan Girka

Ana sa ran cimma daidaito a kan tsawaita shirin ba da tallafin kuɗaɗe ga ƙasar Girka wacce ke barazanar faɗawa cikin wani hali na rashin tabbas idan har ba cimma matsaya ba.

Firaministan na Girka Alexis Tsipras ya buƙaci a ƙara wa'adin tallafin da watannin shida. Sai dai Jamus ta yi karan tsaye kan cewar tilas ne Girkan ta ci gaba da aiwatar da shirin tsuke bakin aljihu kafin samun tallafin na biliyan 240.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman