EU za ta gana kan shirin kwararar baki | Labarai | DW | 18.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

EU za ta gana kan shirin kwararar baki

A shirin da ƙasashen na Ƙungiyar EU ke yi ana son amfani da jiragen yaƙi na sojan ruwa wajen hana fasaƙaurin baƙi da ke neman mafaka a Turai.

A ranar Litinin ɗin nan ƙungiyar ƙasashen Turai EU za ta yi wani zama kan shirinta na yaƙi da masu fasaƙaurin mutane ta tekun Bahar Rum, yayin da ɗaruruwan mutane ke ci gaba da mutuwa a lokacin wannan kasada.

Wanann shiri da zai ƙunshi maƙudan kuɗaɗe da yin amfani da dakarun sojan ruwa daga ƙasashe na EU wanda kuma aka tsara zai fara aiki a watan Yuni, ya hadar da girke jiragen yaki na ruwa da kuma jiragen sinturi da za su riƙa hana masu fasakaurin shiga yankunan ƙasashen ta ruwa bayan sun baro gabar tekun Libya.

Taron na birnin Brussel ana kallon babban ƙalubale da zai fiskanta na zama yadda MDD za ta karɓi wannan shiri .