1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shaidar allurar rigakafin corona

Binta Aliyu Zurmi MNA
March 17, 2021

Shugabannin kungiyar tarayyar Turai za su fidda sabbin shawarwari a kan hanyoyin da za a bi domin samar da katin shaidar allurar rigakafi, da zai ba mutum damar yin tafiye-tafiye muddin ya karbi rigakafin.

https://p.dw.com/p/3ql0G
Symbolbild Immunitätspass
Hoto: Axel Bueckert/Zoonar/picture alliance

Katin da suka ce za a kira shi "Green digital certificate" zai dauki bayyanai da suka hada da cewar mutum ya karbi rigakafin.

Wannan matakin samar da katin dai za a yi shi ne domin bunkasa fannin yawon bude ido wanda tuni ya shiga halin ni 'ya su a sabili da annobar ta corona, abin da zai taimaka wajen farfado da tattalin arziki.

Ana sa ran kasashen da suka fi yawan samun matafiya daga kasashe dabam-dabam na duniya za su fi saurin aminta da wannan matakin, wanda tuni kasashen Italiya da Faransa sun nuna amincewarsu.

Nan da zuwa watan Augusta ake sa ran fara amfani da katin.